Matar Da Tafi kowacce Ƙankanta Ta Yi Aure Tana Shekaru 23


Kamar yadda kundin tattara bayanai kan shahararrun mutanen duniya (Guiness world book of record) ya rawaito, Jyoti Amge ita ce mace ma fi kankanta a duniya. ‘Yar asalin kasar Indiya ce, kuma an haife ta a watan Disambar shekarar 1995. Yanzu tana da shekaru 23 da haihuwa. Jyoty ita ce ke rike da kambun mace ma fi kankanta a duniya.

Ta karɓi kambun tun shekaru shidda da suka gabata wato shekarar 2012. Tsawonta da kadan ya wuce kafa biyu, wato ba ta ma kai girman jariri ɗan shekara guda ba, tirkashi! Allah sarkin halitta. A binciken da likitoci suka yi, rashin tsawon Jyoti yana da nasaba da wata lalura da ke jikinta mai suna ‘Achondroplasia’ wacce take hana ta girma.

Iyayenta sun sha zaryar zuwa asibiti tun tana da shekaru uku don su samo musabbabin abin da ke hana ta girma. Amaryar ta bayyana cewa: Ma fi yawan lokuta takan shiga damuwa idan mutane suka zubo mata na mujiya, wani lokacin ma har rufe fuskarta take idan kallon ya yi yawa. Amma duk da haka ta ce tana alfahari da kankantar tata domin ba ta hana ta yin abubuwan da sauran mutanen duniya masu tsawo suke yi ba. Sai dai mu ce Allah ya ba amarya Jyoti zaman lafiya.


Like it? Share with your friends!

2
77 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like