Matar Atiku ta yi kira ga matan Benue da suyi watsi da Jam’iyar APC


Hajiya Titi Atiku Abubakar uwargidan Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, tayi kira ga matan jihar Benue da su fatattaki jam’iyar APC a zaben ranar 16 ga watan Faburairu.

Matar Abubakar wacce jirgin yakin neman zaben mijinta ya yada zango ranar Litinin a Makurdi ta jaddada bukatar dake akwai na matan jihar da suyi wa mijinta ruwan kuri’a a zabe mai zuwa.

Ta ce jihar karkashin gwamnatin jam’iyar APC a matakin tarayya ta shiga cikin wani mawuyacin hali kusan shekaru hudu kenan musamman ta fuskar tsaro wanda ya yi illa ga mata da kuma matasan jihar.

Ta kara da cewa kada matasa su yarda a yaudare su ta hanyar sayar da ƙuri’unsu kan kudi ₦10,000 inda ta karfafa cewa idan aka zabi mijinta to zai samar da miliyoyin aiyuka ga dumbin matasan da basu da abin yi.

Tun da fari matar gwamnan jihar Benue,Eunice Ortom ta bayyana cewa tuni matan jihar suka yanke shawarar zaben Atiku Abubakar a matsayin shugaban ƙasa da kuma sauran yan takarar jam’iyyar PDP.


Like it? Share with your friends!

-1
84 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like