Mataimakin gwamnan jihar Jigawa zai tsaya takarar sanata


Mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Barista Ibrahim Hassan Hadeja, a jiya Talata ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar sanata a kakar zaɓen shekarar 2019.

Hadeja ya bayyana aniyartasa lokacin da dattawan da suka fito daga kananan hukumomi 8 dake ƙarƙashin masarautar Hadeja suka kai masa ziyarar ban girma a Dutse.

Dattawan sun nemi ya ayyana aniyar tasa ta tsayawa takara.

Shugaban tawagar, Alhaji Umar Mohammed, Magayakin Hadeja ya ce mataimakin gwamnan bawai kawai dan dansu bane, saboda ya wakilci
masarautar na tsawon lokaci ba tare ya basu kunya ba.

Bayan mataimakin gwamnan ya ayyana aniyar tasa dattawan sun yi alkawarin mara masa baya kana suka yi alkawarin aiki tukuru domin samun nasararsa a lokacin zabe.

Mataimakin gwamnan ya godewa gwamna Badaru Abubakar kan goyon baya da kuma haɗin kan da yake bashi ya yin da yake gudanar da aikinsa.


Like it? Share with your friends!

-1
95 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like