Mataimakin gwamnan jihar Edo ya koma jam’iyar PDP daga APC


Mataimakin gwamnan jihar Edo, Agboola Ajayi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar APC.

Ya mika takardar murabus dinsa ga sakatariyar jam’iyar a mazabar Apoi 2 a karamar hukumar Eso Odo ta jihar a ranar Lahadi.

Jim kadan bayan barin jam’iyar mai mulki a jihar Ondo, Ajayi ya wuce sakatariyar jam’iyar PDP dake mazabarsa inda ya yanki katin jam’iyar.

Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da yan sanda suka hana shi fita daga gidan gwamnatin jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like