Mataimakin gwamnan jihar Bauchi,Baba Tela ya warke daga cutar Korona bayan da ya shafe sama da mako guda yana jinya.

Rilwanu Muhammad, shugaban hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko ta jihar shi ne ya bayyana haka ranar Laraba.

Kafafen yada labarai da dama ciki har da Arewa24news sun rawaito cewa mataimakin gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin kar ta kwana na yaki da cutar Korona a jihar ya kamu da cutar.

“Kwanaki 9 da suka wuce mai girma mataimakin gwamna yana killace saboda ya kamu da cutar Korona,”Muhammad ya ce.

“Amma kuma mun gode Allah, bayan kara yi masa wani gwajin yanzu bashi da cutar kuma an sallame shi.”