Wasu mutane bakwai sun jikkata a harin da da wuka da mutumin ya kai a Erfurt babban birnin Jihar Thuringia dake tsakiyar Jamus a yau Litinin, maharin ya tsere sai dai ‘yan sanda sun bi sahun sa da jirgi mai saukar ungulu.

Hukumomi a yankin ba su tabbatar da harin ko yana da laka da ta’addanci ba, sai dai rahotannin ‘yan sandan sun tabbatar da maharin dan asalin kasar Somaliya ne mai shekaru 24 bayan samo bayanai daga wayar salular da aka samu a dakinsa. Wasu bayanai ma na cewa maharin ya taba jinyar matsalar kwakwalwa a shekarun baya.