Mata Sai a Motsa, Dangote Na Buƙatar Matar Aure.


Hamshakin mai kuɗin nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewar yana bukatar macen aure.

Hamshakin ɗan kasuwan ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar “Financial Times” inda ya bayyana cewa tarin sabgogin da ke gabansa ba zasu hana shi kara neman wata abokiyar rayuwar ba.

Mahaifin ‘ya’ya mata guda ukun, wanda ya rabu da matansa na aure sau biyu, ya bada bayanin cewa girma ya kama shi, saboda haka yana bukatar ya kara aure.

Yake cewa: “Girma ya kama ni. Shekaru sittin ba wasa bane. Amma babu ma’ana ace ka fita ka nemi wata abokiyar zaman alhali ba ka da lokaci. A halin yanzu ayyuka sun yi matukar yawa, saboda muna da matatar mai, muna da sinadaran man fetir da iskar gas, muna da takin zamani sannan muna da bututun iskar gas.”

Bagan haka, dattijan mai shekaru 61 ya amince da bukatar ya nutsu, ya samu abokiyar rayuwa ta gaskiya.


Like it? Share with your friends!

-2
118 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like