Dubban masu zanga-zangar nuna takaicin rashin tsaro a jihar Nejan Najeriya, sun kwashe sa’o’i da dama, inda suka rufe babbar hanyar mota da ta tashi daga Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar sun kona tayoyi tare da tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a kan babban titin na Abuja zuwa Kaduna da safiyar yau fitinin inda suka bukaci gwamnatocin jihohi da ma na tarayya su karfafa matakan tsaro tare da kawo karshen yawan hare-haren yan bindiga a yankin.