Masu zanga-zanga daga jihar Kogi sun mamaye ofishin jam’iyar PDP


Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin yakin neman zaben jam’iyar PDP dake Abuja suna zanga-zangar kakaba musu dan takara da aka yi.

Masu zanga-zangar sun ce akwai shirin kakaba musu,Tajuddeen Yusuf a mazabar Kabba/Nuni/Ijumu dake jihar Kogi.

Yusuf shine wakilin dake wakiltar mazabar a majalisar wakilai ta tarayya.

Yusuf ya janye daga takarar majalisar dattawa na yankinsa inda ya goyi bayan sanata Dino Melaye, dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma a zaben fidda gwanin jam’iyar PDP da aka gudanar kana ya shiga zaben fidda gwani na yan takarar majalisar wakilai ta tarayya da ake takaddama akai.

Da yake magana da yan jaridu, Emmanuel Olukade tsohon shugaban jam’iyar PDP na karamar hukumar Ijumu ya ce “yan takara uku aka tantance aka kuma amince su tsaya a zaɓen fidda gwanin na ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2018.”

“Yan takarkaru da kuma daleget sun tattara a otal din Prestige dake Kabba wurin da aka tsara za a gudanar da zaben a wannan rana amma mun jira tsawon a wanni 16 ba tare da ganin wakilan da aka turo su gudanar da zaben ba babu kuma wani dalili da aka bayar na kin halartar su.”

Olukade ya nemi shugabancin jam’iyar karkashin jagorancin Uche Secondus da ya sake gudanar da wani zaben.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like