Masu zaben sarkin Kano sun shiga da karar Ganduje gaban babbar kotun jihar


Masu nada sarki a masarautar Kano sun kai karar gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a gaban babbar kotun jihar inda suke kalubalantar matakin da ya dauka na kirkiro wasu sabbin masarautu hudu a jihar.

A ranar 8 ga watan Mayu ne gwamna Ganduje ya kirkiro karin masarautu hudu a wani yunkuri da mutane da dama suke gani anyi shine domin rage iko da kuma fada aji da Sarkin Kano Muhammad Sunusi II yake da shi.

Masu nada sarkin sunce matakin da gwamnan ya dauka ya sauya tarihin masarauta.

Masu nada sarkin da suka shigar da karar sun hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani; Makaman Kano,Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Maituta,Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai Alhaji Muktar Adnan.

Sauran wadanda mutanen suke kara sun hada da shugaban majalisar dokokin jihar, Kabiru Alhassan Rurum, majalisar dokokin jihar, kwamishinan shari’a na Kano, gwamnan Kano da kuma sabbin sarakunan da aka naɗa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like