Masu Zaben Sarki Sun Maka Ganduje A KOTU


Babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta sanya ranar 17 ga watan nan domin fara sauraron karar da masu nada Sarki suka shigar.

Karar dai na kalubantar kafa sabuwar dokar kafa Masarautu ta 2019 bayan rushe tsohuwar da kotu tayi, an shigar da karar ne ranar 4 ga Disamba.

Jaridar Dabo FM ta rawaiyo cewa, ta ci karo da wata takarda da ta bulla mai lamba SUIT No.K/197/2019, wadda kotu ke sanar da ranar da za ta fara sauraron wannan kara da masu nada Sarkin suka shigar.

Suna zargin cewa a wannan karon ma ba a bi doka wajen samar da masarautun ba, domin kuwa an samar dasu ne duk da umarnin wata kotu da ya hana yin hakan.

Masu shigar da karar sun hada da

Sarkin Ban Kano, Mukhtar Adnan.

Madakin Kano, Yusuf Nabahani.

Makaman Kano, Abdullahi Sarki Ibrahim.

Sarkin Dawaki Mai Tuta, Bello Abubakar.

Wadanda ake kara sune:

Gwamnan Kano

Kakakin Majalisar Kano

Majalisar Kano

Atoni Janar

Aminu Ado

Ibrahim Gaya

Tafida Abubakar Ila

Dr. Ibrahim Abubakar II

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like