Masoyan biyu masu suna Mohammed Alhaji-Musa da Hauwa Yahaya-Bagudu za a daura auren na su ne a yau Juma’a, bayan sun hadu a sansanin su na Kano shekara daya da ya wuce.

Angon dan asalin kabilar Afo ne dake jihar Nasarawa, yayin da ita kuma amaryar ‘yar kabilar Nufe ce dake jihar Neja.