Masu NYSC 731 sun kamu da cutar Korona


Shugaban kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar korona, Boss Mustapha ya ce masu aikin hidimar kasa wato NYSC su 731 cikin mutum 34,418 ne suka kamu da cutar Korona.

Da yake magana a wurin taron ganawa da yan jaridu a ranar Talata, Mustapha ya ce yan NYSC dake fadin kasarnan sun yi gwajin cutar Covid-19.

Ya bayyana cewa wadanda aka samu sun kamu da cutar sun fito ne daga dukkanin jihohin dake fadin kasarnan.

Mustapha wanda shi ne sakataren gwamnatin tarayya ya kuma bayyana damuwarsa kan yawan mutanen da suka kamu da cutar a ranar Litinin.

Mutane 1204 hukumar NCDC dake dakile yaduwar cutuka ta tabbatar sun kamu da cutar wanda shine a dadi mafi da aka taba su a rana tun lokacin da cutar ta bullo Najeriya.

Ya ce an samu yawan karuware masu ɗauke da cutar sanadiyyar tafiye-tafiye da aka gudanar lokacin Kirsimeti


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like