A yanzu dai kimanin kwanaki 10 kenan da wadan nan ‘yan bindiga suk ayi dirar mikiya a garin na Tegina tare da kwashe wadan nan dalibai bayan da suka hallaka mutun guda da rana tsaka.

A wani taron Manema Labarai a makon jiya, Mataimakin Gwamnan jihar Nejan Alh. Ahmed Muhammad Ketso, ya ce duk da ya ke gwamnatin jihar na kokarin kubutar da yaran amma gwamnati ba ta da niyyar biyan kudin fansa ga yanbindigar.

A yanzu dai masu sharhi akan al’amurra na ci gaba da jefa ayar tambaya akan yadda kungiyoyi musamman na kasa da kasa su ke nuna rashin damuwa sosai akan daliban Islamiyah dake daji a hannun ‘yanvbindigar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti: