Masu garkuwa da mutane sun sako tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan Taraba bayan sun karbi miliyan ₦20


Masu garkuwa da mutane sun sako tsohon shugaban ma’aikatan marigayi, Danbaba Suntai tsohon gwamnan jihar Taraba,wanda aka sace kwanaki biyar da suka sace shi.

An sake shi ne ranar Juma’a da daddare bayan da iyalinsa suka biya miliyan ₦20.

Aminu Jika wanda makusanci ne ga gwamnan jihar na yanzu, Darius Ishaku wasu yan bindiga ne da ba’asan ko suwaye ba suka sace shi daga gidansa dake Magami a Jalingo babban birnin jihar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa masu garkuwar sunyi amfani da wayarsa wajen tuntubar iyalinsa, suka kuma bukaci a biya su kudin fansa har miliyan ₦20.

Sun dage cewa dole ne sai an biya kudin a lokacin da suke tattaunawa da iyalinsa inda aka ajiye musu kudin a cikin wani daji.

Wani kaninsa mai suna, Nasiru Bobboji ya ce an sako jika da daddare jim kadan bayan biyan kudin fansar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like