Masu garkuwa da mutane sun sako surukar Masari bayan mako guda tana hannunsu


Sirikar gwamnan jihar Katsina,Aminu Bello Masari ta shaki iskar yanci bayan da ta shafe mako guda a hannun wadanda suka yi garkuwa da ita.

Sirikar gwamnan mai shekaru 80 an sace ta ne daga gidanta dake yankin Sabon Gari a birnin Katsina

A wata sanarwa ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar yansandan jihar Katsina,Gambo Isa ya ce an sako sirikar gwamnan ne a ranar Alhamis.

Isa bai fayyace kan ko anbiya kuɗin fansa kafin a sako ta.

“Ina farin cikin sanar daku cewa sirikar mai girma gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari masu, garkuwa da ita sun sake ta da misalin karfe hudu na yammacin ranar Asabar,”ya ce.

Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa tana cikin koshin lafiya lokacin da aka sako ta.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like