Masu garkuwa da mutane sun harbi manajan Banki suka kuma sace matarsa


Masu garkuwa da mutane sun harbi, Alhaji Muhammad Umar manajan Bankin Manoma na kasa reshen Jalingo babban birnin jihar Taraba a yankin Yagai dake Jalingo inda suka yi garkuwa da maidakinsa Rukayya.

Hakan na faruwa ne duk da dokar hana fita da gwamnan jihar,Darius Ishaku ya saka a birnin Jalingo biyo bayan rikicin da ya barke a wasu unguwannin dake birnin.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa masu garkuwar da yawansu ya kai 10 sun farma gidan da tsakar daren ranar Lahadi.

Masu garkuwar dake dauke da makamai sun kutsa kai dakin kwanan manajan inda suka harbe shi a ciki suka kuma yi awon gaba da maidakinsa.

Sauran mata biyun ne suka ankarar da jama’a abin da ke faruwa amma babu wanda ya kawo musu dauki har zuwa lokacin da masu garkuwar suka tafi.

An gaggauta kai manajan Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Jalingo inda likitoci suka samu nasarar cire harsashin bayan da suka dauki sa’o’i da dama suna yi masa tiyata.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ASP David Misal ya tabbatar da faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

2
85 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like