Gwamnatin jihar Bauchi ta sallami mutane 20 bayan da suka warke daga cutar Korona a jihar.

Gwamnan jihr Bala Muhammad wanda ya bayyana labarin ya ce wannan cigaban da aka samu ya kara yawan mutanen da suka warke daga cutar ya zuwa 89.

Ya zuwa ranar Lahadi an tabbatar da samu karin mutane uku da suka kamu da cutar a jihar abin da ya sa yawan wadanda suka kamu da cutar a jihar ya kai 215.

Jumullar mutane uku aka samu sun mutu sanadiyar cutar a jihar.