Masari: Kaso 99 na yan bindigar da suke addabar Katsina sun fito ne daga Zamfara


Gwamnan jihar Katsina,Aminu Bello Masari ya ce kaso 99 na yan bindigar da suke kai hari jihar sun fito ne daga jihar Zamfara.

Ƙauyuka da dame ne dake jihohi daban-daban a yankin arewacin Najeriya ke fama da hare-hare daga wasu gungun yan bindiga.

Da yake magana da yan jaridu a gidansa dake Kafur a karamar hukumar Kafur ta jihar, Masari ya ce kananan hukumomi uku da suka hada iyaka da jihar Zamfara, sun zamo wani yanki mai hatsari.Ya kara da cewa ayyukan yan bindiga na yin kafar ungulu ga kokarin da yake na dawo da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya ce dole ne sai an yi maganin yan bindigar dake Zamfara idan ana so a samu zaman lafiya a Katsina.

Ya ce bayanan tsaro da yake samu a kowace safiya suna nuna cewa wuraren da ake samun matsalolin tsaro su ne kananan hukumomin, Faskari Sabawa da kuma Dandume.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Очень много граждан сейчас используют online не только для получения информации, сколько для покупок всяческих изделий, которые сейчас просто-напросто заполнили его. Здесь также можно найти запрещенные к продаже и незаконные группы. Только не в обычном поисковом сервисе по типу Яндекса, а в отдельно взятой доменной зоне, знаменитой как Даркнет. Площадкой этой сети интернет и будет hydra сайт, сайт которой мы и разберем во всех подробностях здесь. Поэтому, если для вас тема покупки незаконных изделий актуальна, тогда вам этот материал получится полезен.

You may also like