Maryam Sanda Ta Yi Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Ɗiyar Ta


A jiya Alhamis, Maryam_Sanda ta shirya wa diyarta Dabdalar Maulidi saboda murnar zagayowar ranar haihuwarta. Wannan ya zo daidai da kwana daya kacal da aka ba da belinta.

Maryam dai ana tuhumarta ne da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a sakamakon wata rashin jituwa da ta faru a tsakaninsu.

Kotu ta ci gaba da tsare ta a gidan yari, a yayin da aka yi ta neman belinta sau hudu, amma Mai Shari’a ya hana, sai a shekaranjiya Laraba, Babbar Kotun Abuja ta amince da hujjojin lauyanta, cewa tana fama da mummunar rashin lafiya kuma tana da ciki dan wata uku.

Sai dai kwana daya da ba ta beli, maimakon a ji labarin tana kwance ana mata magani a wani asibiti, sai ga shi ta shirya wa diyarta gagarumar dabdala.
***


Like it? Share with your friends!

1
142 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like