MARYAM SANDA: Duk Abinda Mutum Ya Shuka…


A zahirin yadda abun yake a rayuwa shine: dukkan abunda mutum ya shuka, ko ya shirya wa kan sa, ko ya binne wa kan sa, shine abunda zai girbe. Sakamkon aiki yana ga mai aikata shi.

Babban kotun tarayya dake Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyan rataya. Maryam Sanda idan baku manta ba, ta kashe mijin ta Bilyaminu Bello a ranan 9 ga watan Nuwamba 2017 a gidan su.

Yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa shine abu mafi dacewa da adalci saboda rai ta dauka da cikakken hankalin ta kuma da cikakken niyya. Babu wani hujja da ya wuce wadannan in banda faruwar hakan.

A nan inaso mu fahimci girman laifin da Maryam ta aikata saboda ya zama darasi ga ire-iren ta:

1. Kisa: Maryam ta aikata abu baƙo a cikin al’umman Hausawa musamman mata, kuma ta sunnan ta shi ga masu ra’ayi irin nata.

2. Kisan Miji: a cikin wannan lamari bayan kisan kanshi, matar ta aiwatar da kisan ne a kan mijin ta. Wanann kuma shine mafi girman laifi da mutum zai yi tunani faruwar sa a cikin al’umman mu na Hausa/Fulani. Wannan abu ne da ya saɓawa hankali, tunani, addini, al’ada da dukkan wani abu da ya ginu akan hankali na ɗan Adam.

Mutum yana aure ne saboda ya samu abokiyar rayuwa wacce zata taimaka ma sa wajen gina zuriyar sa da kuma tsayawa tare da shi a halin damuwa ko jin dadi. Amman a zahirin abun, Marigayi Bilyaminu Bello bai samu ko daya daga cikin wadannan abunda na ambata ba sabida kashe shi da matar sa tayi.

Maryam tana da damar ɗaukaka ƙara, kamar yanda alkalin da ya yanke hukunci ya ce. Hukuncin da ya yanke babu shakka shine mafi kusantuwa da adalci saboda bayyanannun hujjoji da aka samu akan mai laifin.

Wannan ishara ce ga duk wata Maryam Sanda. A farkon shekarar da ta gabata kaɗai an samu rahotannin ta’addancin mata akan mazajen su a Arewacin Nijeriya a ƙalla guda 34. Wanda kuma wasu daga cikin su Matan nasu sun aika su lahira. Wasu kuma sun dau lokaci suna fama da jinya saboda rauni da matayen su suka mu su.

Hukuncin kisa ga Maryam alama ne na aiki da tsarin doka akan kowa kuma kwarin gwuiwa ne ga al’umma cewa kotu shine wurin da ake ƙwato wa mai hakki hakkin sa.

Muna addu’a Allah ya jikan Bilyaminu Bello Ya gafarta masa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like