MARTANIN MASARAUTAR KANO GA WASIKAR GWAMNATIN KANO.


Fadar masarautar Kano ta hannun mukaddaahin sakataren masarautar Abba Yusuf, tayi martani ga wasikar da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aika mata.

Wasikar dai ta nemi mai martaba sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu yayi Karin bayani akan zargin almubazzaranci da baitul maliln masarautar da hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe korafe ta jihar Kano keyi masa.

Ga abinda gundarin wasikar ke cewa.

“Bayan ‘yan gaishe gaishe da adireshi da kowacce wasika ta saba kunsa. Da farko dai mai martaba sarki ya gaji Naira biliyan daya da dubu dari takwas da casa’in da uku, da dubu dari uku da saba’in da takwas, da dari tara da ashirin da bakwai da kwabo talatin da takwas ne ba wai Naira biliyan uku da miliyan dari hudu ba da ake zargi.

Sannan yana da muhimmanci ku fahimci cewa bafa mai martaba sarki ne ke da alhakin kula da asusun masarautar Kano ba, sakataren masarautar shine yake da alhakin kula da asusun.

A karshe wasikar tayi godiya ga damar da gwamnatin jiha ta baiwa masarautar Kano domin yin karin bayani akan zarge-zargen da aka bijiro dasu”.


Like it? Share with your friends!

2
68 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like