Manyan Ayyukan Guda 21 da shugaban kasa Muhammadu Buhari Yayi A Yankin Arewa


Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi aiki masu yawan gaske a yankin arewa, amma mun dan binciko muku kadan daga cikin ayyukan shugaban kasar

1. Aikin hanya mafi girma a Najeriya, wacce ta taso daga Kano zuwa Abuja, mai tsawon kilomita 400.

2. Aikin tashar wutar lantarki mafi girma a tarihin Najeriya ta Mambila Hydro Power Station, wacce zata samar da wuta megawatts 3050 idan an kammala.

3. Aikin bincike da kuma hako man fetir a Bauchi da Maiduguri.

4. Tashar jirgin ruwa ta farko a tarihin yankin arewa ta Baro Sea Port dake jihar Niger.

5. Aikin hanyar jihar Kano zuwa jihar Katsina.

6. Aikin hanyar Kano, Bauchi, Potiskum da Borno

7. Ya mayar da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano irin na kasar Turai.

8. Aikin hanyar Bye Pass na jihar Kano. Read

9. Ya gina Jami’ar sojoji ta Biu a jihar Borno, wacce yanzu haka an fara karatu a cikinta.

10. Ya gama aikin tashar wutar lantarki ta Kashimbila dake jihar Taraba.

11. Ya kusa kammala gina tashar wutar lantarki ta Zungeru dake jihar Niger, wacce aka watsar da aikin shekara da shekaru.

12. Ya kammala tashar jirgin kasa wacce ta tashi daga Kaduna zuwa Abuja.

13. Shirin ciyar da yara ‘yan firamare a jihohin Najeriya

14. Ya gina Air Force Base mai girma, da babban asibitin sojoji a jihar Bauchi.

15. Shirin N-Power.

16. Shirin tallafin noma da gwamnati take bayarwa kashi 76 na arewa ne.

17. Aikin titin jirgin kasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Kano, wanda yanzu ake kan yi.

18. Ginin Commodity Market dake karamar hukumar Gezawa jihar Kano.

19. Ya gina Police Academy Secondary School a kafin Madaki dake jihar Bauchi.

20. Ya bayar da naira miliyan 60 ga jihar Kano domin samar da ruwan sha.

21. Aikin hanyar Ganye, Mayo Belwa, da Toungo mai tsawon kilomita 112, wanda yanzu haka an kusa kammalawa a jihar Adamawa.

Wannan kadan ne daga cikin ayyukan shugaban kasar, wanda yayi a yankin nahiyar arewa.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like