Shugaban gwamnatin Kanar Assimi Goita ya furta hakan ne jim kadan bayan rantsardda shi a matsayin shugaban kasar na wuccin gadi a Bamako fadar gwamnatin kasar.

Sabon shugaban dai ya jagoranci juyin mulki a kasar mai fama da kalubalen tsaro har sau biyu cikin kasa da watanni tara, wanda kuma ya sha rantsuwar kama aiki tare da alkawalin sake mayar da kasar bisa tafarkin damakaradiyya.

Juyin mulkin da sojojin suka yi ya janyo wa Malin tabarbarewar harkokin diplomasiyya a fadin duniya, bayan da kungiyoyin ECOWAS da na Tarayyar Afirka ta AU suka dakatar da ita daga cikin su.