Mali: Dakile yunkurin juyin mulki | Labarai | DWA wata sanarwar da ta fitar fadar mulki ta Bamako ta ce ta kama sojin da suka kudiri aniyar mayar da hannun agogo baya a daren 11 zuwa 12 ga wannan watan, tare da zargin wata kasar waje da hannu kai tsaye wajen kitsa makarkashiyar, sai dai kuma gwamnatin bata yi wani karin haske kan kasar da take zargi ba.

Tuni dai mahukuntan na birnin Bamako, suka kara tsaurara matakan tsaro kan iyakokin fita daga babban birnin da ma daukacin iyakokin kasar baki daya.

Tun bayan juyin mulkin da soji suka yi wa wata gwamnatin farar hula ta rikon kwarya a watan Mayun bara, sabbin mahukuntan na Mali suka fada zaman doya da manya wasu kasashen duniya ciki har da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, lamarin da ya kai ga Faransar janye sojojinta da ke yiki da ta’addanci.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg