Malami ya yiwa daliba yar shekara 12 fyade


Wani malami mai suna,Nathan Yusuf ya yiwa wata daliba yar shekara 12 fyade a jihar Adamawa.

Lamarin marar dadi ya faru ne kasa da mako biyu bayan da aka samu kawun wata yarinya yar shekara biyar da laifin yi mata fyade.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar samar da tsaro ta Civil Defence a jihar, Sulaiman Baba shine ya tabbatar da kama Yusuf ranar Laraba.

Ya ce “muna jiran rahoton asibiti da shine zai sa musan matakin da zamu dauka,”

“Rahoton likita shine zai nuna ko za a gurfanar da mutumin da ake zargi a gaban kotu ko kuma akasin haka.”

Tuni aka kai yarinyar da abin ya shafa asibitin kwararru dake Yola domin samun kulawar likitoci.


Like it? Share with your friends!

-1
59 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like