Malaman Jami’ar Bayero Sun Bada Tallafin Kayan Abinci Na Naira Miliyan 5 Ga Yan Gudun Hijira Reshen jami’ar Bayero na kungiyar malaman Jami’i ta kasa,ASUU,yabada gudumawar kayayyaki da darajarsu takai naira miliyan 5, ga mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu a yankin arewa maso gabas.

Shugaban kungiyar ta ASUU  reshen jami’ar Ibrahim Barde wanda ya kaddamar da bada tallafin a Kano, yace  sun bada tallafin ne domin ragewa mutanen radadin wahalhalun da suke fama dasu a sansanonin yan gudun hijira dake yankin. 
” Wannan tallafi wani bangare na gudumawar malaman jami’ar,wadanda ASUU ta nemi su tallafawa yan gudun hijirar, ” yace. 

Barde ya bayyana tallafin a matsayin wani tsari da malaman jami’ar suka kirkiro domin sauran makarantu suyi koyi dashi. 

“Mun fara wannan shirine domin kawo wa wadannan mutane dauki,kuma muna shirin, mu mai da bada tallafin a ko wanne wata. 

 “mutane da yawa basu san munufar ASUU  ba, tunaninsu kawai muna zuwa yajin aiki idan akwai rikici tsakanin mu da gwamnati.

” Amma a wannan karon mun kuduri aniyar tafiya domin rage wahalhalun da yan gudun hijira suke fama dasu a fadin kasarnan. ”

Kayan da aka rarraba sun hada da Shinkafa, Gero, Masara, Taliya,Manja da kuma man Kuli. 

Comments 0

Your email address will not be published.

Malaman Jami’ar Bayero Sun Bada Tallafin Kayan Abinci Na Naira Miliyan 5 Ga Yan Gudun Hijira 

log in

reset password

Back to
log in