Malaman Firamare Da El-Rufai Ya Fatattaka Sun Tabbatar Da Goyon Bayansu Ga Sanata Shehu Sani


Wasu malaman firamari da gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sallama daga aiki sun bayyana goyon bayansu ga takarar dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar da dattawa, Sanata Shehu Sani.

Malaman sun bayyana haka ne a yayin da suka kai wa Sanatan ziyara a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba 5 ga watan Disamba, inda suka yi alkawarin mara masa baya a kokarinsa na zarcewa akan kujerar tasa.

Malaman sun kara da cewa sun yanke shawarar goyon bayansa ne saboda shima ya bayyana damuwarsa da halin da suka shiga a lokacin da aka sallame su daga aiki, da wannan ne yasa suka yanke shawarar rama masa biki su da iyalansu ,yan uwa da masoyansu gabadaya .

Jagoran tawagar tsofaffin Malaman, Alice Ayuba ta bayyana cewa zasu tabbatar da sun mayar da Shehu Sani kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PRP ta hanyar yi masa ruwan kuri’a, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Tace “Mun zo ne da nufin bayyana godiyarmu ga Sanatan bisa kokarin goyon bayan daya bamu a lokacin da aka sallame mu daga aiki, ya jajirce wajen kwato mana hakkinmu, tare da fito da abokan aikinmu da aka kama a wancan lokaci, don haka zamu saka masa abinda yayi mana.”Inji ta.

Da yake jawabi, Sanata Shehu ya bayyana godiyarsa ga goyon bayan da tsofaffin Malaman suka bashi, sa’annan ya jaddada alhininsa ga sallamarsu da gwamnatin jahar Kaduna tayi, sa’annan ya tabbatar musu da cewa zai ci gaba da kokarin kwato musu hakkinsu har sai an mayar dasu aikinsu.

Yace “Abin mamaki ne ace bayan kun kwashe shekaru kuna koyarwa wani yazo ya sallame ku a lokaci guda, bayan kuma kuna da kwarewa, amma rana daya wani yazo yace wai baku iya ba. ina tabbatar muku da cewa hanyar da aka bi wajen sallamarku ba bisa ka’ida bace.“Ina tare daku a wannan gwagwarmayar da kuke yi, ku ci gaba da gwagwarmaya, idan ma ba’a mayar daku yanzu ba, lokaci zai zo da lallai sai an mayar daku.”Inji shi.


Like it? Share with your friends!

-1
142 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like