Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kasafin kudin shekarar 2019


Majalisar zartarwa ta tarayya a amince da daftarin kiyasin kasafin kudin shekara mai zuwa.

Majalisar ta amince da kasafin kudin ya yin wani zama na musamman a yau da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta.Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 10:30 na safe a fadar shugaban kasa dake Abuja ya kawo ƙarshe da misalin karfe daya na rana.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Udom Udoma shine ya sanar da amincewar lokacin da yake zantawa da yan jaridar dake dauko rahoto daga fadar shugaban kasa.

Udoma ya ce majalisar zartarwar zata hada kai da bangaren majalisun kasa domin saka ranar da za a gabatar da daftarin kiyasin kasafin kudin ga majalisun.

Amma kuma yaki yarda ya bada cikakken bayani kan abinda kasafin kudin ya kunsa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like