Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kafa jami’o’i masu zaman kansu 4


Majalisar zartarwar ta tarayya ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda huɗu.

Sanarwar kafa jami’oin an yi tane bayan taron majalisar zartarwar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta a fadar Aso Rock dake Abuja.

Da yakewa yan jaridar dake fadar shugaban kasa jawabi a karshen taron majalisar da ya dauki tsawon sa’o’i biyar,Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce sabbin jami’o’in sune, Jami’ar Dominion dake Ibadan a jihar Oyo , Jamiar Trinity, jihar Ogun, Jami’ar Greenfield dake Kaduna da kuma Jami’ar Westland dake Iwo, jihar Osun.

Ya kara da cewa majalisar zartarwar ta amince da kafa dukkanin jami’o’in hudu bayan da suka cika ka’idojin kafa jami’a kamar yadda tawagar Hukumar Kula Da Jami’o’i ta Najeriya ta gani a ziyarar da takai.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like