Majalisar Wakilan Najeriya, ta nemi Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana a gabanta domin bada bahasi dangane da matakin haramta amfani da shafin sada zumunta na Twitter a kasar.

A ranar Juma’a Mohammed ya sanar da rufe shafin a daukacin kasar, matakin da ya fara aiki wayewar garin ranar Asabar.

Majalisar ta dauki matakin gayyatar ministan ne, bayan da ta koma zamanta a ranar Talata inda shugabanta Femi Gbajabiamila ya umarci kwamitocin da ke kula da sadarwa, shari’a da al’adu, su binciki lamarin tare da gayyatar Lai Mohammed.

“Ina mai bada umarni ga kwamitocin, da su gayyaci Ministan Yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed, don ya bada bahasi a gaban majalisar, kan manufar daukan wannan mataki da kuma iya tsawon lokacin da haramcin zai dauka.” Gbajabiamila ya ce a jawabinsa na bude zaman majalisar.

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamaila (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamaila (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Majalisar ta ce, kamar sauran kafafen sada zumunta, Twitter na da muhimmanci wajen sadarwa da gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya, musamman a tsakanin matasa.

Sai da a cewar Gbajabiamila, “majalisar na sane da cewa, duk da cewa dandalin sada zumunta na da alfanunsa, zai kuma iya zama makami ga masu miyagun manufofi.”

Majalisar mai mambobi 360 wacce ke da rinjayen ‘yan jam’iyya mai mulki ta APC, ta ba kwamitocin kwana 10 su gabatar mata da rahoto kan wannan lamari.

Hukumomin Najeriya sun ce sun dauki matakin rufe dandalin na Twitter ne, saboda bazarana da yake yi ga zaman lafiyar kasar.

A makon da ya gabata, Twitter ya goge wani sako da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa kan masu ta da kayar baya a kudu maso gabashin kasar, saboda ya saba ka’idojinsa.

Dalili kenan da ake ganin ya sa gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani ta hanyar dakile ayyukan dandalin sada zumuntar, lamarin da ya janyo suka da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar.

Alhaji Lai Mohammed (Facebook/Federal Ministry of Information and Culture)

Alhaji Lai Mohammed (Facebook/Federal Ministry of Information and Culture)

Sakon na Buhari da Twitter ya goge, ya yi gargadi ne ga ‘ya’yan kungiyar da ake zargi da kai hare-hare, inda ya ce, gwamnati za ta dauki mataki akan su daidai da abinda ya fi dacewa da su.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Amurka, kungiyar Tarayyar Turai, da Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty duk sun soki matakin rufe kafar ta Twitter.

Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna alamu na goyon baya ga kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra, wacce hukumomin kasar suka haramta a shekarar 2017.