Majalisar wakilai ta dage dakatarwar da ta yi wa Abdulmumin Jibrin


Majalisar wakilai ta tarayya ta janye dakatarwar da ta yi wa Abdulmuminu Jibrin wakili daga jihar Kano dake wakiltar al’ummar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar.

Hakan ya biyo bayan wasikar ba da hakuri da Jibrin ya rubutowa majalisar a ranar Talata.

Majalisar ta dakatar da Jibrin na tsawon kwanaki 180 na zaman majalisar bayan da ya fallasa cewa an yi karin wasu aiyuka da kudinsu ya kai biliyan ₦30 a cikin kasafin kudin shekarar 2016.

Lokacin da aka dakatar da shi ɗan majalisar shine shugaban kwamitin kasafin kudi na  majalisar.

Shugaban majalisar Yakubu Dogara shine ya sanar da wasikar bada hakurin a zaman majalisar na ranar Talata.

Duk da bai karanta abinda wasikar ta kunsa ba Dogara ya ce dan majalisar zai iya dawowa idan yana so.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like