Majalisar wakilai ta amince da 12 ga watan Mayu a matsayin ranar dimakwaradiya


Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar bikin dimakwaradiya.

Yan majalisar sun nuna amincewarsu ne ranar Alhamis ya yin da suke duba kudurin gyaran dokar ranakun hutun ma’aikata.

Gyran dokar ya zama dole bayan da shugaban kasa Muhammad Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimakwaradiya.

Buhari ya yi hakan ne domin tunawa da, marigayi MKO Abiola mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Kafin gyaran dokar ranar, 29 ga watan Mayun kowace shekara ita ce ranar bikin dimakwaradiya a Najeriya.


Like it? Share with your friends!

-1
95 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like