Majalisar wakilai ta amince Buhari ya nada masu bashi shawara 15


Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da bukatar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya aika mata dake neman a sahale masa ya nada masu bashi shawara 15.

Sahalewar ta biyo bayan amincewa da majalisar tayi da kudurin shugaban masu rinjaye,Alahsan Ado Doguwa ya gabatar a zauren majalisar ya yin zamanta na ranar Alhamis.

Yin hakan da majalisar tayi ya yi dai-dai da sashe 151(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Sashen ya ce shugaban kasa nada ikon ya nada kowane mutum a matsayin mai bashi shawara domin ya taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya,NAN ya rawaito cewa shugaban kasar a wani sako da ya aikewa majalisar ranar 9 ga watan Yuli ya nemi sahalewar majalisar domin ya nada mutane masu bashi shawara 15

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like