Majalisar dokokin jihar Katsina ta yi sabon shugaba


Mamba dake wakiltar mazabar Zango a majalisar dokokin jihar Katsina,Tasi’u Musa Maigari ya zamo sabon shugaban majalisar dokokin jihar.

An zabi Maigari ya maye kujerar kakakin majalisar dokokin jihar, bayan da tsohon kakakin majalisar, Abubakar Yahaya Kusada ya sauka daga mukaminsa sakamakon tsaben da aka yi masa na dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ingawa/Kusada/Kankia a majalisar wakilai ta tarayya.

A zaman majalisar na ranar Litinin Kusada ya sanar da murabus dinsa inda akawun majalisar ya sanar da cewa babu kowa akan kujerar kana ya nemi da a cike gurbin da kakakin ya bari.

Mamba mai wakiltar karamar hukumar Matazu shine ya gabatar da kudirin tsaben sabon kakakin inda ya samu goyon bayan, Sani Lawal mamba mai wakiltar mazabarBaure daga nan ilahirin majalisar dokokin ta amince.

Sabon kakakin ya dage zaman majalisar ya zuwa ranar 14 ga watan Janairu.


Like it? Share with your friends!

-1
70 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like