Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amincewa Ganduje Ya Karbo Bashin Naira Bilyan 15


Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbo bashin banki bilyan goma sha biyar (N15bn) domin inganta harkar Ilimi a kananan hukumomin jihar 44.

Majalisar ta tabbatar da bukatar ne a ranar Laraba a zaman da kakakin majalisar, Alhaji AbdulAzeez Garba-Gafasa ya jagoranta.

Za ku tuna cewa a ranar Talata, kakin majalisar ya karanta wasikar gwamna Ganduje na bukatar dama ga kananan hukumomi 44 amsan bashi daga hannun banki.

Yan majalisan sun bayyana amincewarsu bayan mataimakin shugaban masu rinjaye, Alhaji Kabiru Hassan-Dashi ya gabatar da rahoton kwamitin.

Kwamitin ta bayyana cewa za’a yi amfani da kudin ne wajen ajujuwa da gyara wasu domin rage cinkoson yara a makarantun gwamnati.

Hassan-Dashi ya kara da cewa za’a yi amfani da kudin wajen dinkawa dalibai sabbin kayan makaranta da kuma inganta shirin ciyar da yara da gwamnatin jihar ta kaddamar.

A bayanin da Ganduje yayi a wasikar, ya bayyana cewa za’a baiwa kowace karamar hukumar cikin 44 na jihar N340 million domn inganta ilmi a jihar.

Hakazalika ya ce sharadin bashin shine za’a biya cikin watanni 30 na kudin ruwan kashi 15 cikin 100.

Za’a rika cire kudin ne cikin kudin da gwamnatin tarayya take baiwa kananan hukumomi kowani wata.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like