Majalisar dokokin jihar Imo ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar


Majalisar dokokin jihar,Imo ta fara zaman tsige mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumare.

A zaman majalisar na ranar Talata, Ugonna Ozuruigbo, mataimakin shugaban majalisar ya gabatar da kudirin fara shirin tsige Madumare.

Ana zargin mataimakin gwamnan da kauracewa aikinsa na tsawon lokaci da kuma kin yin wasu aiyukan gwamnati da gwamnan ya neme shi ya yi.

Majalisar ta kafa wani kwamiti mai wakilai shida karkashin jagorancin, Kennedy Ibe , mamba dake wakiltar karamar hukumar Obolo da ya binciki zarge-zargen kana ya mika rahotansa cikin kwanaki bakwai.

Tun da farko, Acho Ahim kakakin majalisar ya dakatar da wani dan majalisar wanda ya soki yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

Madumare ya dade yana takun saka da gwamnan jihar, Cif Rochas Okorocha tun bayan da ya nuna sha’awarsa ta darewa kujerar mulkin jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like