Majalisar dattawa zata shirya taro kan sha’anin tsaro


Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce majalisar zata shirya karin babban wani taro da zai tattauna matsalar tsaro da ta addabi kasarnan.

Ahmad ya bayyana haka ranar Talata lokacin da yake magana kan kudiri da abokan aikinsa suke mahawara akai.

Ayo Akinyelure, sanata dake wakiltar mazabar Ondo ta tsakiya shine ya jawo hankalin majalisar kan kisan da aka yi wa Funke Olakunrin yar gidan, Reuben Fasoranti shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere.

Taron da aka shiryawa gudanarwa na zuwa ne watanni 14 bayan da majalisar dattawa ta 8 karkashin jagorancin Abubakar Bukola Saraki ta gudanar irinsa.

Shawarwari ashirin aka amince da su bayan da kwamitin wucin gadi da aka dorawa sa’ido akan taron ya gabatar da rahotonsa.

Da yake gabatar da kudirin,Akinyelure ya ce jami’an tsaro basa abin da ya dace wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da ita.

Sanatan ya ce yan Najeriya da dama suna jin basu da kariya akan tituna saboda yawan hare-haren da suke faruwa.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
72 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.