Majalisar dattawa ta tabbatar da Nami a matsayin shugaban FIRS


Majalisar dattawa tabbatar da nadin da aka yi wa, Muhammad Nami a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya, FIRS.

Majalisar dattawan ta tabbatar da nadin da aka yi wa, Nami a ranar Laraba bayan da ta karbi rahoton kwamitin kudi na majalisar.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa, Muhammad Buhari ya nemi majalisar dattawan da ta tabbatar nadin mukamin da aka yi wa Nami.

Nadin na Nami ya zo ne biyo bayan cikar wa’adin shugabancin ,Tunde Fowler

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like