Majalisar dattawa ta nemi gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta ɓaci kan rashin aikin yi


Majalisar dattawa ta nemi gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta baci kan rashin aikin yi.

Hakan ya biyo bayan kudurin da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, sanata Ike Ekweremadu ya gabatar a zauren majalisar.

Da yake gabatar da kudirin tsohon mataimakin majalisar dattawan ya bayyana halin da ake ciki na rashin aikin yi a matsayin wani bam da ka iya fashewa a kowane lokaci.

Ya ce kalaman ministan kwadago da nagartar aiki, Chris Ngige da jaridar Premium Times ta wallafa ya nuna cewa a dadin marasa aikin yi zai karu da kaso 33.5 cikin dari a shekarar 2020.

Ya kara da cewa dukkaninsu a matsayinsu na wakilan jama’a babban bukatar da ake gabatarwa a wurinsu shine tarin takardun neman aiki daga mutanen mazabunsu da suke wakilta.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like