A taron gaggawa da majalisar ta kira kan tabarbarewar tsaro a wasu kananan hukumomin jihar, majalisar ta bayyana fargabar rashin tsaron na iya bazuwa zuwa wasu sassan Jihar, idan har ba’a dauki matakan da suka dace wajen dakile shi ba.

Shugaban majalisar, Farfesa Pandang Yamsat ya ce dole sai an zakulo bata- gari da ke ci da sunan addini suke kuma hada baki da makiya daga waje, wurin halaka jama’a da lalata dukiyoyinsu.

Shi ma shugaban majalisar, mai martaba Sarkin Wase Muhammadu Sambo Haruna ya jaddada muhimmancin hadin kai ne tsakanin ‘yan majalisar.

Sakataren gwamnatin Jihar Filato, Farfesa Danladi Atu ya ce gwamnati ta sayo babura don gaggauta kai agaji a lunguna.

A baya Gwamna Simon Lalong, ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a duk fadin jihar.

Ya kuma jaddada cewa, ba zai lamunci a rika cewa wasu mahara da ba a san ko su waye ba a duk lokacin da aka kai hari a wasu sassan jihar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: