Mutumin nan da ake zargi da kai wa shugaban rikon kwaryar kasar Mali Assimi Goita hari da wuka ya mutu a hannun hukumomi, a cewar sanarwar da mahukuntan kasar suka fidda. Mutumin da har ya zuwa wannan lokacin ba a fayyace ko wane ne ba, wanda tun bayan harin ake tsare da shi, an sanar daga baya cewa ba shi da lafiya wanda har ta kai shi ga kwanciya a asibiti, daga bisani ya ce ga garinku nan. Sanarwar ta kara da cewar ana kan gudanar da bincike domin sanin musabbabin mutuwar ta shi.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai aka kai wa shugaban kasar ta Mali hari da wuka a masallacin Idi.Kasar ta Mali da ko baya ga rikicin siyasar da take fama da shi wanda ya jefa kasar ga juyin mulki har sau biyu, tana fama da rikicin ta’addanci.