Mahara sun kashe sojin Najeriya 30 a Niger | Labarai | DWRahotanni majiyoyin tsaro a Najeriya, na cewa akalla sojojin kasar 30 sun mutu a wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga su ka yi musu a yankin Shiroro na jihar Neja a farkon mako mai karewa.

Sojojin na cikin jami’an tsaron da aka tura domin neman ma’aikatan hakar ma’adinai da aka sace a ranar Laraba, ciki har da ‘yan kasar China hudu.

Babu tabbacin kungiyar da ta kai wannan mumunar hari a kauyen Ajata Aboki da ke jihar Niger a arewa maso yammacin Najeriya, sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Asabar cewa ” ‘yan bindigar ‘yan bakin ciki ne, kuma za su fuakanci hukunci. Mazauna Shiroro za su ga adalci.”
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg