Mutane wadanda suka kai harin a daran Juma’a wayewar Asabar sun kone kasuwar garin kurmus tare da kashe mata da yara da mazaje wanda ake tsamanin adadin zai iya zarta dari. Wannan dai shi ne hari mafi muni da ‘yan ta’addar suka kai a Burkina Faso tun bayan harin da ya afku a shekara ta 2015. A halin da ake ciki gwamnatin ta ce ta tura sojoji domin bin sawun  wadanda suka aikaita ta’asar.