Mahara a jihar Taraba sun fatattaki Jukunawa mazauna kauyen Rafin Kada


Wasu mahara da ake zaton sun fito ne daga wata kabila sun kai hari garin Rafin Kada dake jihar Taraba inda suka kashe mutane da dama.

Rafin Kada gari ne na yan kabilar Jukun dake kan hanyar Takum-Wukari ya kuma fuskanci hari da safiyar ranar Talata daga wasu da ake zargin mayaka ne.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa mayakan sun shigo garin ne daga jihar Benue mai makotaka da jihar inda suka kashe mutane masu yawa tare da kona gidaje.

Sun kuma kai farmaki kan motar shugaban karamar hukumar Wukari da kuma wata mota dake dauke da sojoji da suka nufi Rafin Kada bayanda suka samu kiran kai daukin gaggawa.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Mista Adi Daniel ya fadawa jaridar Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa mayakan sun kaddamar da harin kan Rafin Kada yau da safe.

Ya ce an kashe wasu mutane ya yin da maharan suka kona gidaje sama da 30.


Like it? Share with your friends!

-1
89 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like