Magu:Bankin FCMB ya muslta tura kudi asusun Godwin Omale


Bankin FCMB ya musalta zargin dake cewa an turawa wani makusancin, Ibrahim Magu tsohon shugaban hukumar EFCC kudi har naira miliyan 573.

A watan da ya gabata ne shugaban kasa, Muhammad Buhari ya dakatar da Magu kana ya bada umarnin a bincike shi a tsawon shekarun da ya shafe yana rikon mukamin shugaban hukumar.

Akwai dai rahotannin dake cewa manajan bankin FCMB,Adam Nuru ya fadawa kwamitin binciken Magu, cewa an saka miliyan 573 bisa kuskure cikin asusun, fasto Godwin Omale.

Amma mai magana da yawun FCMB, Diran Olojo ya ce babu wani lokaci da aka tura kudi cikin wannan asusu da ake fada.

Olojo ya ce abin da aka samu shi ne tangardar na’ura kuma hakan ya nuna a bayanan hukumar NFIU mai binciken hada-hadar kudade a bankuna.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like