Magoya Bayan PDP Su 536 Sun Sauya Sheka Zuwa APC A Jihar Jigawa


Wasu Matasa Da Dattijai ‘Yan Jam’iyyar PDP Su 536 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC A A Kauyen Gari Uku, Mazabar Dunari Dake Karamar Hukumar Malam madori.

Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa Kuma Dan Takarar Sanata Na Shiyyar Jigawa Arewa Maso Gabas Wato Barista Ibrahim Hassan Hadejia (Shattiman Hadejia) Ne Ya Karbe su.

Barista Ibrahim Hassan Ya Bada Tabbacin Cewa Jam’iyyar APC Za ta Rike su Ba Tare da Nuna Bambanci ba.

Daga Karshe Mutanen Garin Sun Bada Tabbacin Baiwa Jam’iyyar APC Dukkanin Kuri’unsu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like