Magoya bayan Mama Taraba 5000 sun koma jam’iyyar APC


Sani Abubakar Danladi, dantakarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam’iyyar APC ya karbi mambobin jam’iyar UDP sama da mutane 5000 dama yan wasu jam’iyu dake jihar da suka sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

Masu sauya shekar da suka hada da shugabannin jam’iyar a matakin ƙananan hukumomi da kuma mazabu tunda fari sun fita daga jam’iyar inda suka bi tsohuwar minitan mata,Hajiya Aisha Alhassan ya zuwa jam’iyar UDP.

Da yake karɓar masu sauya shekar ranar Asabar a Jalingo, Abubakar ya ce an kawo karshen dukkanin rikici da kuma sabanin da ya biyo bayan zaben fidda gwani tun da hukumar zabe ta wallafa sunayen yan takara.

Ya roki dukkanin yan jam’iyar da su hada kai domin fuskantar kalubalen dake gabansu na samun nasarar jam’iyar a 2019.

Dantakarar gwamnan ya ce jam’iyar ta fara shirin sasantawa ta hanyar tuntubar sauran yan takarar gwamna da ba suyi nasara ba a zaben fidda gwani.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like