Magoya bayan jam’iyar APC sun tayar da tarzoma a Bayelsa


Wasu magoya bayan jam’iyar APC sun gudanar da zanga-zanga biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar.

Yayan jam’iyyar ta APC sun farma gidan rediyon jihar inda suka fasa motocin aiki da wasu kayayyaki.

Har ila yau fusatattun mutanen sun rika kona tayoyi tare da fadin basa son wani gwamna sai, David Lyon.

A jiya ne kotun koli ta umarci hukumar zabe ta INEC da ta janye takardar shedar cin zabe da ta bawa , David Lyon na jam’iyar APC ta kuma bawa dan takara na biyu da yafi samun kuri’u a zaben sabuwar takardar shedar cin zabe.

Kotun koli ta samu dan takarar mataimakin gwamnan jihar da laifin amfani da takardun bogi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like