Magoya bayan Buhari sun yi fada a birnin tarayya


Wasu daga cikin magoya bayan shugaban kasa, Muhammad Buhari sun yi fada da juna a dandalin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja.

An shirya cewa matasan da suka fusata za su halarci taron wata kungiya dake neman shugaba Buhari ya sake tsayawa takara a shekarar 2018.

Rikicin ya fara ne lokacin da jagororin shirya taron suka fara rabon kyautttuka ga mahalarta taron.

Wasu sun koka kan cewa wadanda aka dorawa alhakin rabon ba su yi adalci ba.

Yunkurin shawo kan mutanen yaci tura ya yin da suka cigaba da doke-dole a tsakaninsu tare da cifa da muggan abubuwa.

Manyan baƙin da suka halarci tarom sun gudu saboda kan rikicin ya rutsa da su.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like